Gwamnatin Katsina tare da haɗin gwiwar shirin samar da ruwan sha na Bankin Duniya za su kashe Naira Biliyan 20 domin samar da ingantaccen ruwan sha a jihar.
Kwamishinan ma’aikatar ruwa na jihar, Bishir Gambo Saulawa ne ya bayyana haka a wani taro da manema labarai.
Kwamishinan ya ce, gwamnatin jihar ta sa Naira miliyan dubu biyar, Bankin kuma ya sa miliyan dubu sha biyar a kashin farko na aikin.
Ana sa rai za a kammala aikin a ƙasa da watanni shida a yankunan ƙananan hukumomi 10.
Shugaban Hukumar Samar Da Ruwan Sha Da Tsaftar Muhalli a Karkara, Abubakar Sulaiman Abukur ya ce, za a samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana masu ɗauke da tankunan ruwa mai lita dubu takwas a ƙauyuka arba’in a karkashin Shirin.