Bankin CBN ya ce za a ci gaba da amfanin da tsaffin kudi
Babban bankin kasa CBN, ya ce ba za a daina amfani da tsaffin takardun kudi na naira 1000 da 500 da 200 ba.
A wata sanarwa da bankin ya fitar, wanda muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na bankin Sidi Ali Hakama ya fitar, ya ce labarin da ake yaɗawa kan wa’adin amfani da tsaffin takardun kuɗin ba gaskiya ba ne.
Bankin ya kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa na cewa daga ranar 31 ga watan Disamban nan za a daina amfani da tsaffin kuɗin.
Gidan Talabijin na Channels ya rawaito Hukuncin da Kotun Ƙolin kasar nan ta yanke a ranar 29 ga Nuwamban 2023, ta amince a ci gaba da amfani da sababbi da tsofaffin takardun kuɗaɗen naira.