Jam’iyyar PDP ta ce ba ta ji dadin ficewar tsohon gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa daga cikinta ba.
Babban Mataimaki Na Musamman ga shugaban jam’iyyar kan harkokin labarai, Yusuf Dingyadi ya ce, ba sa jin dadin wannan samun raguwa a cikin jam’iyyar ba.
“Sai dai babu yadda za mu yi domin tilas jam’iyya ta hakura, musamman ganin dokar kasa ta ba shi damar yin haka.
“Attahiru Bafarawa bai nuna cewa akwai wata matsala a PDP ba, da ta yi silar ficewarsa, saboda haka ba za mu ce rikicin jam’iyya ne ya sa ya fice ba”. inji shi
Tsohon gwamnan na jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya ayyana ficewarsa daga PDP ba tare da bayyana cewa an yi masa wani laifi ba.
Bafarawa ya bayyana hakan ne cikin wata wasika da ta bulla a kafafen yada labari a ranar Talata 14 ga watan Janairun 2025, wadda ya sanya wa hannu da kansa.
A cikin wasikar ficewa daga jam’iyyar, wadda ya rubuta wa shugaban jam’iyyar na kasa a ranar 8 ga watan Janairu, Bafarawa ya ce: “Na rubuto wannan takarda domin gabatar da matakin ficewa daga jam’iyyar PDP”.
A watannin baya an ga Bafarawa da Hajiya Naja’atu a wani bidiyo suna jagorantar tarukan matasa a karkashin wata kungiya a arewancin Najeriya.