
Kwankwaso da Shekarau (Hoto shafin BBC)
Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekaru ya ce, babu wani sabani tsakaninsa da Rabiu Musa Kwankwaso dake bukatar a sasanta su.
Shekarau ya fadi haka ne a ranar Juma’a a ma matsayin martani ga masu ikirarin kokarin sasanta tsakaninsu.
Tsohon gwamnan ya kuma ce, yana da kyakkyawar alaka tsakaninsa da jagoran jam’iyyar NNPP ba kamar yadda ake yadawa ba.
“Babu wata tattaunawa da nufin sulhu tsakanina Kwankwaso, sabanin rahotannin da ke cewa za a sulhunta mu.
“Ni ban ma yarda a yi amfani da kalmar sulhu tsakanina da ɗan’uwana Rabiu Musa Kwankwaso ba.”
“Duk inda ka ji an ce sulhu, to rigima ake yi. Ba na rigama da shi, ba ya rigima da ni, muna gaisawa cikin mutunci da kuma ziyartar juna idan akwai sanadi.
“Muna magana da yan’uwantaka da juna tsakanina da Kwankwaso,” in ji Shekarau a hirarsa da BBC.
Tsoffin gwamnonin biyu na Kano Malam shekarau da Rabiu Musa Kwankwaso sun taba zama inuwa daya a jam’iyyar APC da kuma NNPP ta Kwankwaso kafin Shekarau ya fice daga jam’iyyar.
Wasu rahotanni kuma na alakanta sasanci ne tsakanin ɓangarorin biyu domin buƙatun siyasa.
Aminu Sulen Garon ne ya fara kawo batun sasanta tsaffin gwamnonin na Kano, Kwankwaso da Ganduje da kuma Shekarau a ‘yan watannin baya.
Sai kuma Sanata A.A Zaura ya sake yin Magana kan batun a makon jiya yana mai cewa suna kokarin sasanta tsaffin gwamnonin domin ci gaban siyasar jihar.