
Gwamnan Neja Mohammed Umaru Bago ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa akwai saɓani mai girma tsakaninsa da mataimakinsa, Yakubu Garba, inda ya ce babu abin da ke tsakaninsu sai dai fahimtar juna da girmama juna.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya karɓi karramawar gwarzon ma’aikata a bikin Ranar Ma’aikata da aka yi a Minna.
A cewarsa batun barakar duk raɗe-raɗi ne kawai ake yaɗawa domin babu abin da zai iya shiga tsakaninsu.
Bago ya samu rakiyar Sanata Mohammed Sani Musa ne, wanda yake wakiltar Neja ta Gabas a majalisar dattawa.
Sai dai ya ce wasu ayyukan masu muhimmanci ne suka sa mataimakinsa bai samu damar halartar bikin ba.