Duk da rade-radin da ke yawo cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da faruwar hakan.
A ‘yan kwanakin nan ne jita-jitar ta bazu a fadin jihar Kano, inda ake alakanta gwamnan da yunkurin ficewa daga jam’iyyar NNPP, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan siyasa, magoya bayan jam’iyyun siyasa da kuma al’ummar jihar baki ɗaya.
Rade-radin sun kara daukar hankalin jama’a ne musamman bayan da aka samu karuwar jami’an tsaro a kofar gidan gwamnatin Kano a safiyar ranar Litinin.
Jami’an tsaron sun tsaurara matakan bincike ga duk masu shiga da fita, lamarin da ya janyo hankalin jama’a da masu wucewa a yankin.
Sai dai wasu ‘yan siyasa da mazauna birnin Kano sun bayyana cewa tsauraran matakan tsaron ba lallai ne su kasance da nasaba da batun sauya sheka ba.
A cewarsu, matakan na iya kasancewa sakamakon muhimman taruka ko kuma tsare-tsaren tsaro na yau da kullum domin kare lafiyar gwamnan da sauran manyan jami’an gwamnati.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar Kano ko jam’iyyar NNPP da ke tabbatar da sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa wata jam’iyya.
