Babbar Cibiyar Wutar Lantarki ta Ƙasa ta koma aiki bayan lalacewar da ta yi tsawon Litinin, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a sassan ƙasar.
A wata sanarwa da cibiyar ta fitar a daren Litinin, ta bayyana cewa an shawo kan matsalar tare da dawo da tsarin samar da wutar lantarki yadda ya kamata.
Cibiyar ta ce tsarin ya faɗi ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Litinin.
A cewarta, matsalar ta samo asali ne daga lalacewar bututun iskar gas da ke Legas a ranar 10 ga watan Disamba, wanda hakan ya janyo ƙarancin iskar gas da ake kaiwa cibiyoyin samar da wutar lantarki.
Katsewar wutar lantarkin ta faru ne kwana guda kacal bayan Gwamnatin Tarayya ta sanar da kammala gyaran babbar cibiyar lantarki ta ƙasa da ke Legas.
