
Ya ce, a lokacin sun fahimci hatsarin mika mulki ga farar hula ne shi ya sa suka dauki wannan mataki
Babangida ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Alhamis, yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna ‘A Journey in Service’.
Babangida ya amsa alhakin soke zaɓen da aka gudanar tsakanin Moshood Abiola na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da Bashir Tofa na jam’iyyar National Republican Convention (NRC).
“Ina nadamar soke zaɓen ranar 12 ga watan Yuni. Na ɗauki alhakin matakin da aka ɗauka, domin hakan ya faru ne a ƙarƙashina ikona.
“Mun yi kuskure, kuma abubuwa sun faru cikin gaggawa,” in ji Babangida.
Aminiya ta rawaito cewa, tsohon shugaban na mulkin soja ya taɓa kare matakin soke zaɓen, inda ya ce, an gudanar da shi cikin gaskiya da adalci.
A cewarsa wancan lokaci, Najeriya ba ta shirya karɓar mulkin dimokuraɗiyya ba ya kuma ce, zaben na 12 ga watan Yuni shi ne zaɓe mafi kyau a tarihin Najeriya, an kuma yi shi cikin gaskiya da adalci. Amma abin takaici dole suka soke shi.
“A lokacin, mun fahimci hatsarin miƙa mulki ga gwamnatin dimokuraɗiyya. Mun yi tsoron cewa idan muka miƙa mulki, cikin watanni shida, wani juyin mulki zai sake faruwa, kuma hakan zai zama gazawa a ɓangarenmu,” in ji shi.
Babangida, ya ƙara da cewa bayan soke zaɓen, gwamnatinsa ta shirya gudanar da wani sabon zaɓe a watan Nuwamban 1993. Amma saboda tarzomar da ta biyo bayan soke zaɓen, ba a samu damar yin wani zaɓen ba.
A cewarsa a maimakon haka, sun kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, amma daga baya, Janar Sani Abacha ya hamɓarar da ita.
Taron wanda aka yi otal din Transcorp, ya samu halartar manyan ‘yan siyasa da sauran masu rike da mukamai gwamnati.