
Gwamnatin Iran ta musanta zargin da Isra’ila ke yi mata na kai hare-haren makamai masu linzami bayan sanarwar tsagaita wuta da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a matsayin matakin dakile rikicin da ya dauki kwanaki 12.
A cewar kafar yada labarai ta Iran, sojojin kasar sun ce ba su harba wani makami zuwa Isra’ila ba tun bayan sanarwar tsagaita wutar, suna mai cewa zargin Isra’ila wata hanya ce ta neman uzurin ci gaba da kai farmaki.
Sai dai Isra’ila ta dage cewa Iran ta karya yarjejeniyar inda ta ce an harba makamai daga Iran zuwa arewacin Isra’il, lamarin da ya jikkata mutum ɗaya, kamar yadda hukumomin lafiya suka tabbatar.
Ministan Tsaron Isra’ila Israel Katz ya bayyana cewa ya umurci rundunar sojin kasar da su mayar da martani da karfi, tare da kai mummunan farmaki kan cibiyoyin gwamnatin Iran a tsakiyar Tehran.
A nata bangaren Iran ta ce ba za ta dakatar da martaninta ba har sai Isra’ila ta daina kai hare-hare, tana mai cewa ba a cimma cikakkiyar yarjejeniya ba kan tsagaita wutar da Trump ya sanar ba.