Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce, kasarsa ba za ta yarda da wata yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka da Rasha suka cimma ba matuƙar ba a sanya ta cikin tattaunawar ba.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, ya za su tattauna da Vladimir Putin, inda suka amince su fara shawarwari don kawo ƙarshen yaƙin.
Zelensky ya jaddada cewa, Ukraine ba za ta karɓi kowace matsaya da Rasha ta tsara ba.
Shugaban na Ukraine ya kuma ce bai tattauna batun NATO da Trump ba, amma yana da masaniyar cewa Amurka ba ta goyon bayan shigar Ukraine cikin ƙungiyar.
Trump zai gana da Putin a Saudi Arabia kan yaƙin, amma Fadar White House ta nuna babu shirin bai wa wata ƙasar Turai, ciki har da Ukraine, damar halartar taron.
