
Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ta musanta zargin daukar nauyin tarwatsa taron tsaro da wasu matasa suka yi.
A sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Dakta Bala Salisu Zango, ya fitar ranar Talata, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da nesanta gwamnatin jihar daga zarge-zargen cewa tana da hannu a wargaza taron.
“Gwamnatin ma ai ta halarci irin wannan taro da aka gudanar a Abuja a kwanakin baya, sannan Kuma za mu ci gaba da yin aiki tare da hukumomin tsaro da shugabannin al’umma da Kuma sauran masu ruwa da tsaki domin kawo karshen matsalar tsaro a jihar.” In ji Kwamishinan.
Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun tarwatsa taron da dattawan Katsina suka shirya don tattauna matsalolin tsaro da ke addabar jihar a farko makon Nan.