Gamayyar Tsofaffin Jami’an da suka yi aikin Hisbah a Kano sun bayyana rashin goyon bayansu ga yunkurin kafa Hisba mai zaman kanta a jihar. Wannan yunkuri yana da mahimmanci wajen tabbatar da #hisba a Kano.
Tsaffin ma’aikatan karkashin Jagorancin Farfesa Mu’azzam Mai Bishra ne suka bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a yammacin Alhamis.
“La’akari da yanda matsalolin tsaro suka fara kunno kai jihar Kano, yunkurin na Ganduje ba komai zai haifar ba illa fitina da ƙara rura wutar rikici tsakanin al’ummar Kano.” In ji shi.
Taron ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta waiwayi koken ‘ƴan Hisbar da aka kora a kwanan nan.
A cewar Farfesan, bayanai sun nuna da yawa an kore su ne ba tare da bin ƙa’idojin korar ma’aikata ba.
Sannan ya yi kira ga gwamnatin Kano da ta waiwayi matsalolin Hukumar Hisbar ta hanyar samar musu da kayan aiki na zamani domin ayyukansu su ci gaba yadda ya kamata.
