Fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da zargin wasu ’yan adawa na amfani da EFCC wajen cin zarafi da musguna musu.
Ta kuma musanta zargin cewa dimokuraɗiyya na cikin barazana saboda sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC da ake yi.
Hakan na cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi.
“Wasu ‘yan siyasar adawa na yin surutu ne kawai saboda gazawarsu a siyasa.
“EFCC na da ’yancin cin gashin kanta bisa doka, kuma tana gudanar da aikinta ba tare da tsoma bakin kowa ba.
Fadar shugaban ƙasa ta kuma yi kira ga ’yan siyasar da ake bincike da su tsaya su kare kansu a gaban doka idan sun san ba su da laifi, maimakon yin zarge-zargen siyasa
