
Daga Khali Ibrahim Yaro
Kano ita kadai ta samu tan 50 na dabinon a matsayin gudunmawar kasar ga Najeriya da kuma kyautata dangantaka.
Jakadan Saudiyya a Najeriya Ambasada Al-Ghamdi ne ya mika dabinon a wani biki a ofishin jakadancin kasar a Abuja a ranar Litinin.

Shirin rarraba Dabinon, Cibiyar Bayar Da Agaji Da Ayyukan Jin Kai ta Sarki Salman ce ta dauki nauyin sa domin tallafawa iyalai masu rauni a fadin kasar da kuma karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.
Jakadan sarkin mai kula da masallatan Haramai biyu a Najeriya ya bayyana cewa, rabon na wannan shekarar bana ya hada da tan 50 na dabino ga Abuja da kuma wani tan 50 na jihar Kano
Ya kuma ce, wannan shirin zai ci gaba a bisa al’adar Saudiyya na taimaka wa Najeriya ta hanyar bayar da agaji.