Yara da yawa ne suka mutu sakamakon turmutsutsi a wani dandalin wasan yara mai zaman kansa a jihar oyo.
Lamarin ya faru ne a wani filin wasa mai zaman kansa na makarantar ‘Basorun Islamic High School’ da ke Ibadan babban birnin jihar.
Kwamishinan Labarai da Wayar da Kan Jama’a Prince Dotun Oyelade ya tabbatar da faruwar al’amarin,
Ya Kuma ce gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa, sun kai yaran da suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a birnin Ibadan.
Gwamnatin jihar ta ce, ba ta da hannu wajen shirya taron.
Sannan ta Kuma jaddada mahimmancin haɗa kai wajen shirya manyan bukukuwa, musamman waɗanda suka shafi yara da manya masu shekaru.
Ana dakon cikakken rahoto daga kwamishinan ‘yansanda domin tabbatar da adadin waɗanda suka mutu a wannan mummunan al’amari.