
Kwamishinan ‘Yan Sanda na birnin tarayya Abuja ya bayyana irin kokarin rundunar take yi na tabbatar da tsaro birnin.
Hakan ya biyo bayan mutuwar watan Mai Gabatar da Labarai a tashar Talbijin ta Arise TV A ranar 1 ga Oktoba, 2025.
‘Yar jaridar Somtochukwu Christelle Maduagwu da aka fi sani da “Sommie”—‘yar shekara 29, mutuwarta a birnin.
‘Yar jaridar ta gamu da ajalinta ne a lokacin wani fashi da makami a gidanta da ke yankin Katampe a Abuja a ranar 29 ga Satumba, 2025,
Hakan ya sa hukumomin tsaro suka dauki mataki cikin gaggawa, a bayanin Kwamishinan ‘Yansandan birnin CP Ajao S. Adewale.
“A safiyar ranar 29 ga Satumba, wasu gungun ‘yan fashi da makamai, aƙalla mutum 14, sun mamaye gidan Maduagwu. A cewar abokan aikinta, Ojy Okpe da Reuben Abati a shirin The Morning Show na Arise TV, cikin firigici ‘yar jaridar ta yi tsalle daga barandar gidan don Tsira da ranta ta kuma ji wani babban rauni duk da cewa ta tsere daga hare-haren farko.
“’Yan sanda sun je wurin lamarin kuma suka tarar da ita a kwance cikin mawuyacin hali. Nan take aka garzaya da ita zuwa baban asiibitin Maitama, inda likitoci suka zo kanta cikin gaggawa da CPR, amma rai yayi halinsa . In ji Kwamishinan.
Ya kwatanta harin a matsayin “babban laifi” ya kuma jaddada ‘aniyar ‘yansanda na kare lafiyar jama’a.
Sai dai abokan aikinta sun bayyana wani abin takaici, inda suka ce an ƙi karbar Maduagwu a wani asibiti saboda rashin kudi, hakan yana daga cikin matsala da ake yawan fuskanta a tsarin kiwon lafiya na Najeriya.
Wannan ya haifar da cece-kuce, tare da kira da a sake fasalin don tabbatar da samun kula da gaggawa ba tare da shinge ba.
CP Adewale ya ba da umarnin gudanar da bincike kan yanayin fashin da mutuwar Maduagwu. Haka ma shugaba Tinubu bayyana rashin jin dadin wannan al’amari, kuma ya umarci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike “cikin gaggawa kuma mai zurfi.