Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi tir da kutsen da jami’an tsaro suka yi wa Majalisar Dokokin Jihar Legas, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin ƙi da barazana ga dimokraɗiyya.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bukaci gaggawar gudanar da cikakken bincike kan lamarin, yana mai cewa hakan ba abu ne da za a lamunta da shi ba.
Lamarin ya biyo bayan tsige tsohon shugaban majalisar, Mudashiru Obasa, tare da zaɓen Mojisola Meranda a matsayin sabuwar shugaba.
Jiya Litinin, jami’an tsaro sun kewaye majalisar, inda wani bidiyo ya nuna sun toshe kofar shiga, yayin da ‘yan majalisa suka taru a waje.
