
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jagoran adawa Atiku Abubakar ya ɗauki nauyin karatun dalibai mata 3 da suka yi nasara a gasar Turanci na duniya .
Daliban ‘yan asalin jihar Yobe da Nafisa Abdullahi da Rukaiya Mohammed Fema da Khadija Kashim Kalli sun doke ‘yan uwansu dalibai na duniya a harshen Ingilishi ta TeenEagle Global Finals da aka yi kasar Ingila
Hakan na kunshe a cikin wani saƙo da ya Atikun ya wallafa a shafukan sada zumunta a ranar Alhamis yayin da daliban suka kai masa ziyara a gidansa da ke Abuja, babban birnin tarayya.
A farkon watan Agusta ne matasan ‘yan asalin jihar Yobe suka doke takwarorinsu 20,000 daga sassan duniya a gasar bayan sun wakilci Najeriya daga makarantar Tulip International College.
Gwamnatin tarayya kuma ta dauki data daga cikinsu ta bata N200,000 ta kuma kyale sauran ‘yan kawanaki kadan da ta ba ‘yan wasa kwallo miliyoyin naira wanda ya janyo cece-ku-ce.