
Babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya, PDP, ta mayar da martani kan ficewar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar daga cikin jam’iyyar, inda ta bayyana cewa wannan mataki ba zai haifar da giɓi a cikinta ba.
Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Ibrahim Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin hirarsa da BBC.
“Atiku na ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan da ke haddasa rikice-rikice da rashin jituwa da suka daɗe suna addabar jam’iyyar.” In ji shi
A baya-bayan nan ne Atiku Abubakar ya sanar da ficewarsa daga PDP, yana mai cewa jam’iyyar ta kauce daga asalin tsarin da ya ja hankalinsa a da.
Ya kuma ce, wannan mataki na fita daga PDP ya biyo bayan tsunduma da ya yi cikin haɗakar jam’iyyun adawa ƙarƙashin jam’iyyar ADC, domin shirin tunkarar babban zaɓen 2027.