
Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya bukaci rundunar ƴansandan Najeriya ta gaggauta sakin ɗan fafutikar nan Omoleye Sowore ko ta gurfanar da shi a gaban kotu.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Obi ya bayyana damuwarsa kan matakin da ƴansandan suka ɗauka na ci gaba da tsare Sowore.
”Ina mamakin yadda za a ci gaba da tsare mutumin da ya kai kansa domin amsa gayyatar da ƴansanda suka yi masa”, in ji shi.
Haka zalika shima tsohon dan takarar shugaban kasa a Jamiyyar PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar ya buƙaci a gaggauta sakin Omoyele Sowore da ke tsare a hannun ’yan sanda.
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, wanda ya yi Allah-wadai da lamarin ya ce abin kunya ne cin zarafin da tawagar sa ido ta sufeto janar na ’yan sandan ƙasar suka yi wa Sowore.
Wasu rahotanni ma na bayyana cewa ana zargin ’yan sandan sun lakaɗa wa Sowore duka har ma an ƙarya masa hannu.
Atiku ya ce wannan abin da ƴa nsanda suka aikata ba ga Sowore kaɗai ba ne, inda ya ce hakan ya nuna cewa za a far wa kowane ɗan Najeriya da ya yi ƙoƙarin fitowa ya faɗi gaskiya.
Tuni dai Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta Amnesty International ta fitar da sanarwar Allah wadai da kamun da aka yi wa Sowore wanda ta ce ya saba wa ‘yancinsa na fadin albakacin baki
Haka kuma, Amnesty International ta bukaci a saki Omoleye Sowore nan take ba tare da gindaya masa wasu sharuda ba.