Karamin ministan gidaje, Yusuf Abdullahi Ata, ya yi wa tsohon gwmanan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwason martanin cewa ya daina kalaman da za su raba kan kasa.
Martanin nasa ya biyo bayan kalaman Kwankwason, da ya ce yankin Lagos yana yunƙuri mai ƙarfi na mallake Arewacin Najeriya.
Ko da yake Kwankwaso bai ambaci sunayen mutanen yankin na Lagos da yake zargi suna neman yi wa Arewa mulkin mallakar ba, sai dai wasu na gani yana magana ne game da shugaban kasa Bola Tinubu wanda tsohon gwamnan Lagos ne kuma babban mai faɗa a ji a yankin Kudu Maso Yamma.
Yayin bikin yaye ɗaliban Jami’ar Skyline da ke Kano a ranar Lahadi, Kwankwaso ya ce hakan ne ya sa wasu mutanen yankin na Lagos suka tsoma baki a harkokin masarautar jihar Kano inda suka hana gwamnatin jihar zaɓen sarkinta.
Kwankwaso ya ce a yanzu, Lagos ta hana su zaɓen Sarkinsu shi ya sa Lagos din ta shigo har tsakiyar Kano ta saka nata sarkin.
Ya kuma zargi gwamnatin tarayya da yunƙurin durƙusar da harkokin kasuwanci a Arewa ta hanyar fito da sabuwar dokar haraji.
Sai dai karamin ministan gidaje Yusuf Abdullahi Ata ya yi wa Kwankwason martanin cewa ya daina kalaman da za su raba kan kasa.
Ata ya nuna damuwa kan yadda ya ce kalaman Kwankwason ka iya yamutsa hazo tare da dumama yanayin siyasar kasar nan.
Cikin wata sanarwar da mai taimaka masa kan labarai Adamu Aminu ya fitar a jiya Lahadi, Ata ya kuma yi kira ga Kwanwason da ya dinga jinjina irin kalaman da zai furta saboda tasirinsu ga al’umma.
Ya ce maimakon haka gara ya mayar da hankali wajen tattaunawa domin warware matsalolin da kan taso.
Ya ce a matsayinsu na shugabanni suna da hakkin tabbatar da zaman lafiya da kaucewa kalaman da ka iya jawo tunzuri ko tashin hankali.
Kusan watanni 10 kenan dai ana dambar kan wanene sarkin Kano tsakanin Muhammad Sanusi II da Aminu Ado Bayero tin bayan da majalisar dokokin Kano ta tsige Aminu Ado tare da dawo da Muhammad Sanusi.
Sai dai Alhaji Aminu Ado ya dawo Kano inda ya tare a gidan Sarki na Nassarawa yana zaman fada a matsayin sarki tare da kalubalantar tsige shin a kotu.
Wannan ta sa har kawo yanzu ake ci gaba da dambar wa kan sarautar, da ya janyo kotuna yanke hukunce-hukunce masu cin karo da juna.