
Zazzafar muhawara ta tsawon awanni ta barke a majalisar dokokin Kano biyo bayan fitar wasu bayanai da suka bankado adadin kudurin da kowane dan majalisa a zauren ya gabatar a shekarar 2024
Cikin wani bayaani da Premeie Radio ta samu, akawun majalisar Bashir Idris Diso ne ya fitar da bayanan ga tashar Freedom Radio a cikin wani shiri da majalisar ta dauki nauyin gabatarwa a tashar,
Kunshin bayanan ya nuna aikin kowanne dan majalisawanda hakan kuma ya fallasa zaman dumama kujera da galibin ‘yan majalisar ke yi, wanda hakan ya janyo nuna yatsa tsakanin majalisar da kafar tashar Radion da ta yada.
Kididdigar ayyukan ya nuna cewar Kakakin majalisar Jibril Isma’il Falgore da mataimakinsa Muhammad Bello Butu-Butu na daga cikin mambobi 7 da ba su gabatar da koda kuduri daya ba a shekarar 2024.
Kunshin bayanan sun nuna cewa Dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Rano Ibrahim Muhammad Malami shine wanda ya fi gabatar da kuduri a zauren majalisar a shekara ta 2024, inda ya gabatar da kuduri 18.