
Jam’iyyar APC ta sanar da shirinta na gudanar da taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) a ranar 24 ga watan Yuli, domin yanke shawara kan ko Ali Bukar Dalori zai ci gaba da zama shugaban rikon jam’iyyar ko kuma a nada sabon shugaba.
Wannan mataki ya biyo bayan murabus da tsohon shugaban jam’iyyar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi inda ya bayyana buƙatar mai da hankali kan kula da lafiyarsa a matsayin dalilin sauka daga kujerar.
Bayan ganawa da shugaban ƙasa da kuma jiga-jigan jam’iyyar an amince da Dalori wanda ke matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa maso gabas a matsayin shugaban riko.
Mataimakin Sakataren jam’iyyar na ƙasa Festus Fuanter ne ya bayyana cewa taron na NEC zai ba jam’iyyar damar tantance matsayin Dalori da kuma yiwuwar zaɓen sabon shugaban ƙasa na jam’iyyar.
Ya kuma ce ,an riga an aika da sanarwar taron zuwa Hukumar INEC domin tabbatar da sahihancin tsarin.
Taron na APC zai gudana kwana guda bayan jam’iyyar hamayya ta PDP ta shirya nata taron a ranar 23 ga watan Yuli lamarin da ke nuna ƙayatarwar siyasa da ke tafe a cikin watan.
A halin yanzu, Dalori ya bayyana aniyarsa ta jagoranci jam’iyyar da gaskiya da haɗin kai da kuma ciyar da ita gaba, tare da jinjina ga gudunmawar Ganduje.