Jam’iyyar APC ta nada gwamnan jihar Imo Hope Uzidinma a matsayin shugaban kwamitin mai mambobi 73, sai gwamann Kwara Abdurrazaq Abdurrahman mataimaki da kuma gwamnan Yobe Maimala Buni a matsayin Sakatare.
Akwai gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da kuma wasu gwamnoni da yan majalisun tarayya da sauran jiga jigan APC a matsayin mambobi.
Wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa Surajuddeen Ajibola Basiru ya fitar ta kuma bayyana kudin sayen form ga masu bukatar mukamai daban daban a jam’iyyar tun daga matakin mazaba zuwa kasa.
Sanarwar ta ce wanda ke son tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar na kasa zai biya naira miliya 10, yayin da mai neman mataimaki ko sakatare zai biya naira miliyan 7 da dubu 500.
Sanarwar tace wanda ke neman shugabancin jam’iyyar a matakin mazaba zai biya kudin form naira dubu 20.
APC ta ce za ta gudanar da babban taronta kasa a watan Maris din shekarar 2026.
