Tsohon Ministan Shari’a, Cif Michael Aondoakaa, ya yi kira ga gwamnatin Amurka da ta fadada hare-haren da take kaiwa kan ‘yan ta’adda zuwa Jihar Benue, domin kawar da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda da ke addabar yankin.
Aondoakaa ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manyan ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki a Makurdi, babban birnin jihar Benue, wanda ya gudana a safiyar Asabar.
Tsohon Babban Lauyan ya ce yin wannan kira ya zama dole sakamakon karuwar ayyukan ‘yan ta’adda a sassan jihar Benue.
Wannan kira nasa ya biyo bayan hare-haren sama da Amurka ta kai a wasu sansanonin kungiyar IS a dajin Bauni da ke Jihar Sokoto, wanda aka kai a daren ranar Kirsimeti.
A cewarsa, ya kamata a ce an fara irin wadannan hare-hare ne a Benue tun da dadewa, kafin a kai su zuwa Sokoto.
Ya koka da cewa wasu kananan hukumomi da dama sun fada hannun wasu kungiyoyi masu dauke da makamai, wadanda a cewarsa ke fakewa da sunan makiyaya.
