Ofishin Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta jihar Katsina, ce ta gudanar da gangamin domin tunawa da ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a ranar Litinin
Shugaban Hukumar Dr. Salisu Musa, a jawabinsa a taron ya ce, Hukumar ta shirya taron ne domin jin koken al’umma da bin hakkin waɗanda aka zalunta a ɓangarori daban-daban.
Hukumar na irin wannan gangamin wayar da kan al’umma a duk shekara domin fadakar da su.
Taron gangamin an fara shi ne daga ofishin Magajin Garin Katsina, har zuwa babban ofishin hukumar.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware 10 ga watan Disambar kowacce shekara a matsayin ranar ‘Yancin dan Adam ta duniya.