
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja, na nuna cewa wani mummunan lamari ya faru a Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, inda aka ce jami’an ‘yan sanda sun karya hannun dama na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC) a zaɓen 2023, Omoyele Sowore.
Lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis, lokacin da wata tawaga daga Sashen Bin Diddigi na ofishin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, ƙarƙashin jagorancin wani CSP, suka kutsa ɗakin da aka tsare Sowore, suka fitar da shi da karfi, lamarin da ya jawo karyewar hannun damansa.
A cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafin Instagram na Sowore, an bayyana cewa bayan karye masa hannu, jami’an sun ɗauke shi zuwa wani wuri da ba a bayyana ba, lamarin da ke haifar da ƙarin damuwa kan lafiyarsa da kuma inda yake a halin yanzu.
Jaridar Daily Post ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an tsare Sowore tun ranar Laraba bayan ya amsa wata gayyata daga rundunar ‘yan sanda.
Har yanzu hukumomin ‘yan sanda ba su fitar da cikakken bayani kan dalilan tsarewar ba, haka kuma babu wata sanarwa daga ofishin Sufeto Janar kan zargin cin zarafi da duka da aka yi wa ɗan gwagwarmaya da ya shahara wajen kare haƙƙin ɗan adam da adawa da cin hanci da rashawa.