
Kungiyar kare hakkin Dan Adam ta kasa da kasa (Human Right Network) ta koka kan rawar da shugabar Karamar Hukumar Tudun-Wada, Hajiya Sa’adatu ta taka a rikicin da ya barke tsakanin kananan ‘yan kasuwa makera da ‘yan barandar siyasa a kan batun rusau.
Shugaban Kungiyar kwamared Haruna Ayagi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai kan lamarin a Kano a karshen makon nan.
A cewarsa, rikicin ya yi sanadiyyar raunata wasu ‘yan kasuwar tare da Harbin daya daga cikinsu.“Lallai jami’an tsaro su yi bincike na gaskiya domin nemo wadanda suke da hannu a ciki.
Domin binciken da muka yi ya tabbatar mana da faruwar lamarin. Kuma muna bukatar da a tabbatar da adalci akan wadannan masu sana’a”. In ji Kwamared Ayagi.
Wakilinmu Premier Radio ya tuntibi shugabar karamar hukumar ta Tudun-Wada, Hajiya Sa’adatu Salisu, sai dai wayarta bata shiga, sannan bata bada amsar gajeren sakon da aka tura mata ba.
Takaddamar dai ta fara ne a ranar Alhamis lokacin da Hajiya Sa’adatu ta bayar da umarnin rusa shagunan masu sana’o’i da nufin gina magudanar ruwa.