Masana da masu harkar rubuce-rubuce a ɓangaren sufurin jiragen sama sun zargi Rasha da kakkaɓo jirgin nan na kamfanin sufurin jiragen sama na ƙasar Azerbaijan, wanda ya yi hatsari ranar Laraba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 38.
Babu dai wata hujja da suka bayar, amma sun ce shingen kariya daga makamai na Rasha ne ya yi zaton cewa jirgin maras matuƙi ne na ƙasar Ukraine.
Wasu da suka shaida hatsarin sun bayyana cewa sun ji ƙarar fashewa, sannan kuma hotuna da aka ɗauka na tarkacen jirgin sun nuna wasu ramuka a jikin jirgin da ka iya zama wuraren da makami ya huda.
A lokacin da ya yi magana da manema labarai, mai magana da yawun gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov ya ce bai kamata a riƙa yin shaci-fadi ba.
