
Kotu ta yankewa matashin da ya kashe masallata 23 ta hanyar zuba musu fetur da cinna musu wuta a masallachi hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Babban Kotun Shari’ar Musulunci dake zamanta a Kano ce ta yanke wa Shafi’u Abubakar hukuncin kisa a zaman da ta yi a ranar Litinin bayan ta tabbatar da matashin ya aikata laifin da ake zarginsa.
Kotun ta kuma ce a yiwa mai laifin bulala 150 na cinna wa masallaci wuta da kisan masallata 23 sannan gwamnati ta sayar da mashin dinsa maikafa uku a gyara masallacin da kudin.
Kafin yanke hukuncin, Lauyan Gwamnati Mai Gabatar Da kara Salisu Tahir ya ce, wanda ake zargi ya aikata laifin ne a kauyen Gadan a Larabar Abasawa ta Karamar Hukumar Gezawa ta jihar Kano a ranar 15 ga watan Mayun shekarar 2024.
A inda mai laifin ya je masallacin da misalin karfe 5:05 zuwar 5:15 na asubahin ranar ya watsawa masallatan Fetur ya kuma cinna musu wuta.
An garzaya da masallatan 23 zuwa Asibitin Kwararru na Murtala a cikin birnin Kano a inda wadanda aka kai suka mutu.
Mai laifin Shafi’u Abunbakar ya amsa laifinsa.
Alkalin kotun Malam Khuza’I Zakariyya ya ba mai laifin makwanni 3 na daukaka kara.