An tsinci gawar wata ɗalibar aji ɗaya a Jami’ar Taraba da ke Jalingo (TSU), a ranar Juma’a a cikin ɗakin saurayinta, lamarin da ya tayar da hankali daliban a jami’ar.
Ɗalibar mai suna Comfort Jimtop, ’yar ƙaramar hukumar Takum ce, kuma tana karantar fannin koyon aikin jarida.
Rahotanni sun ce bayan an gano gawarta bayan mazauna gidan suka tsere.
Kakakin rundunar ’yansandan Jihar Taraba, ASP Leshen James, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce suna neman saurayin tare da sauran mazauna gidan da suka tsere.
Ya ƙara da cewa ’yansanda za su gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru da Comfort.
Lamarin ya haifar da firgici da damuwa ga ɗalibai da mazauna yankin.
