An samu cigaba a bangaren tsaro a kasar nan sabanin ‘yan shekarun baya, domin a wasu yankunan manoma sun fara koma wa gonakin su.
Hakan ya fito ne daga bakin Abdulaziz Abdulaziz Mai Taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai musamman a jaridu, a yayin hirarsu da wakilinmu a Abuja.
Tsohon dan jaridan ya kuma ce, an samu karuwar zaman lafiya a yankin Shinkafi a jihar Sakkwato da wasu sassa na jihar Neja a inda yanzu manoma ke komawa gonakin su sabanin baya. Inji shi.
Wani karin nasara da gwamnatin ta samu na baya-bayan nan shine fatattakar gungun ‘yan ta’adda da ake kira Lakurawa da suka bulla a jihar Sakkwatto, suka kuma addabi jihar da makwabciyarta Kebbi da kashe-kashe da kuma satar Dabbobi.
A wani ikikrari da Hekwatar Tsaro ta Kasa ta yi ta ce, Jiragen yakin sojin sama sun ragargaji ‘yan ta’addan a inda suka fattake su daga jihohin.
A kuma wasu lokuta daban-daban rundunar Soji sun sanar da nasarar kisan ‘yan ta’adda a wurare daban-daban a dazukan arewancin kasar da kuma kubutar da mutane da yawa da aka yi garkuwa da su.
Sai dai duk da haka ana cigaba da samun kalubalen tsaro a wasu yankuwan arewacin kasar da ma wasu jajihohin kudancin kasar, wanda su ma a hankali za a kawo karshensu. Inji shi.