An nada tsohon sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Ibrahim M. Ida, wazirin Katsina, a matsayin shugaban kwamitin gudanarwar na hukumar yi wa kamfanoni rajista Corporate Affairs Commission (CAC).
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya nada shi inda matakin ya samu yabo daga babban jami’in yin rajista kuma shugaban hukumar CAC, Hussaini Ishaq Magaji, wanda ya bayyana sanatan a matsayin wanda ya dace da mukamin.
Magaji ya ce Ida na da gogewa mai zurfi a harkokin gwamnati da kasuwanci, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta ayyukan hukumar da kuma karfafa sauye-sauyen da ake aiwatarwa.
A cewarsa, nadin ya yi daidai da manufofin gwamnatin Tinubu na kawo gyare-gyare da inganta ayyukan hukumomi a karkashin shirin Renewed Hope Initiative.
Sanata Ida, wanda aka haifa a 1949, ya taba zama dan majalisar dattawa, sannan ya rike mukamin kwamishinan kudi a jihar Katsina, tare da yin aiki da gwamnati har ya kai matsayin babban sakatare kafin ritayarsa.
Ana sa ran kwarewarsa za ta taimaka wajen bunkasa ayyukan hukumar ta CAC da kuma kara inganta huldarta da sauran kamfanoni.
