
An nada Dakta Bashir Aliyu Umar a matsayin sabon shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da majalisar ta fitar yau Laraba.
Sanarwar wacce Nafiu Baba Ahmed ya sa hannu ta ce, an amince da shugabancin Dakta Bashir ne kai-tsaye saboda kasancewarsa mataimakin shugaban majalisar.
“Nan gaba za a sanar da mataimakin shugaban,” in ji sanarwar da Nafiu Baba Ahmed ya sanya wa hannu a matsayin sakataren majalisar.
Aminiya ta rawaito cewa, naɗin na zuwa ne bayan rasuwar shugaban Majalisar Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah a ranar Litinin a Jihar Osun.
Sheikh Bashir sanannen malami ne kuma shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke Alu Avenue a Unguwar Nasarawa ta Jihar Kano.
Dakta Bashir sha-kundum ne a fagen ilimin shari’a da harkokin kuɗi da kasuwanci bisa tafarkin addinin Islama.
Ya yi digirin digirgir a fannin Hadisi da ilimin addinin Islama a Jami’ar Musulunci ta Madinah.
Shehun Malamin ya yi aiki kwamitoci daban-daban da harkokin kuɗi da Shari’ar Musulunci a ciki da wajen kasar nan, ciki har da kwamitin mashawarta a Bankin Stanbic IBTC da da Majalisar Ƙwararru kan harkokin banki a tsarin addinin Islama da kuma Babban Bankin Nijeriya CBN.