‘Yan sandan kasar sun yi nasarar harbe 30 da cikin 500 na fursonin ne yayin farutar su.
Akalla fursunoni 1,500 ne suka tsere daga babban gidan yarin Maputo daidai lokacin da aka shiga rana ta uku ta tashe-tashen hankali da ya barke.
Babban Baturen ‘ yansandan kasar Bernardino Rafael ya ce, an kashe 33 daga cikin fursunonin yayin da 15 suka jikkata, an kuma samu nasarar kama 150.
A jawabin shugaban a taron manema labarai ya ce, da sauran rina a kaba.
“Akwai fargabar karuwar manyan laifuka, kuma al’amarin ka iya ta’azzara rashin tsaro cikin kwanaki masu zuwa.”
inji shi A ranar Laraba ne wasu gungun masu zanga-zangar da ke kalubalantar sakammakon zaben shugaban kasa suka tunkari babban gidan yarin Maputo wanda hakan ya haifar da rudani da kuma hayaniya,
Ya kma yi sanadiyyar fasa wata katanga da ta sa fursunonin suka tsere.
Da yawa daga fursunonin da suka tsere na da alaka da kungiyoyi masu ikirarin jihadi da suka shafe shekaru bakwai su na ta’addanci a lardin Cabo Delgado d ke arewacin kasar