
Gwamnatin Tarayya ta sanar da kammala tantance sunayen mutanen da za a nada jakadun Najeriya a ofisoshin diflomasiyyar kasar guda 109 a kasashen duniya.
Wannan tsarin na hada da ofisoshin jakadanci guda 76, ofisoshin babban jakada guda 22, da kuma ofisoshin hulda da jama’a guda 11 a kasashe daban-daban.
Majiyoyi daga cikin gwamnati sun tabbatar da cewa an kammala binciken tsaro da duba tarihin kowanne daga cikin wadanda aka mika sunayensu, don tabbatar da cewa za a samu ingantaccen wakilci ga Najeriya a kasashen waje.
A wata tattaunawa da Premier Radio, masanin alakar kasa da kasa, Isma’il Ahmad, ya bayyana cewa rashin jakadan Najeriya a wasu kasashe na daga cikin babbar illa ga kasar.
Ya ce, rashin aika jakadun na nuna cewa Najeriya ta rage kimarta a idon kasashen waje, wanda hakan zai kawo cikas wajen samun damar yin hulda mai inganci da wasu kasashe.
A watan Satumbar shekarar 2023, shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi wa dukkanin jakadun kasar nan kiranye, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin al’umma.
A cewar Ministan ma’aikatar harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar, tsaikon nada jakadu na faruwa ne sakamakon yawan kudin da ake bukata wajen inganta kayayyakin ofisoshin jakadanci da sauran abubuwan da suka shafi gudanarwa.
Ana sa ran gwamnatin za ta kashe akalla Dala biliyan daya wajen gyara da saita ofisoshin jakadanci na Najeriya a kasashen duniya domin tabbatar da cewa suna gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Kamar yadda aka saba, wannan matakin yana nuni da kokarin gwamnatin Najeriya wajen inganta wakilcinta a duniya, musamman ma a fannin diflomasiyya da alakar kasa da kasa.