Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama mutane uku da ake zargi da fashi da makami tare da kwato wata mota da aka sace a Abuja.
kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar YAU Laraba, 10 ga Satumba, 2025.
Sanarwar ta ce an kama su ne a wani samame da aka gudanar tare da haɗin gwiwar jami’an sa-kai, inda aka gano motar kirara Toyota Corolla da aka sace.
