
Wani jami’in ‘yan sanda ya shiga hannun hukuma bisa zargin kashe wani soja a kauyen Futuk, karamar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi.
Daraktan labarai na rundunar soja ta 33 Artillery Brigade, Atang Hallet Solomon, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’in da ake zargi ya harbe sojan har lahira, kuma yanzu ana tsare da shi yayin da ake gudanar da bincike tsakanin ‘yan sanda da sojoji.
Hallet ya kara da cewa ana tattaunawa tsakanin manyan hukumomin tsaro domin tabbatar da cikakken bincike da kauce wa tashin hankali.
A cewar masu farauta da ‘yan banga a Futuk, hatsaniyar ta taso ne daga sabani tsakanin jami’an tsaro kan wata motar kamfanin hakar ma’adinai na kasar Sin, wacce ke dauke da ma’adanai daga rukunin hakar ma’adinai na Yalo.
Motar an tare ta ne da yammacin Litinin bayan sallar Magariba.