
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da cafke wasu mutane biyu bisa zargin safarar muggan makamai daga jihar Jigawa zuwa Katsina.
Kwamishinan Tsaro da Kula da Al’amuran Cikin Gida na jihar, Nasir Mu’azu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
“ ‘Yansandan da ke sintiri a Karamar Hukumar Ingawa ne suka kama wata mota ƙirar maƙare dauke da makamai masu yawa. Binciken ‘yansanda ya nuna cewa motar ta tashi ne daga garin Hadejia a jihar Jigawa, tana nufin zuwa karamar hukumar Safana a jihar Katsina.” In ji shi.
Kwamishinan ya kuma kara da cewa, Daga cikin makaman da aka samu a motar akwai Babbar bindiga mai jigida da Alburusan bindigar AK-47 guda 1,063 da kuma Alburusan bindigar PKT guda 232.