
Shirin bunkasa ilimin ‘ya’ya mata na Gwamnatin Kano da tallafin Bankin Duniya (Agile), ya kaddamar da tsarin koyarwa na tafi da gidanka, watau Mobile Class ga ‘ya’yan Fulani mata.
Sabon tsarin zai bai wa ‘ya’yan Fulani damar samun ilimin addini da na zamani a duk inda suka tsinci kansu. In ji Mustapha Aminu shugaban shirin a jihar.
“Tsarin ajujuwan zai ba su damar su koyi karatu a duk inda yake da haske rana”. In ji shi.
Shugaban ya kuma bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki don ciyar da ilimin ‘ya’yan Fulani mata gaba.
A jawabin shugaban kungiyar Fulani ta FULDAN reshen jihar Kano, Sani Adamu Dakata, yawaitar tafiye-tafiye da fulani ke yi ne yasa ‘ya’yan su basa samun Ilimi yadda yakamata.
Ya kuma ce tsarin ajin na tafi da gidanka, idan an yi amfani da shi yadda ya dace, ‘ya’yan Fulani mata za su samu ci gaban da ake bukata a bangaren Ilimi.