Yansanda a sun gano wata motar ofishin mataimakin gwamnan Kano, da aka sace a harabar gidan gwamnati.
Majiyoyi daga fadar Gwamnatin Kano sun ce an sace motar ce cikin dare.
Lamarin da ya kai ga tsare direban da motar ke hannunsa, a matsayin ɗaya daga cikin wadanda ake zargi.
A sanarwa da ofishin mataimakin gwamnan ya fitar a ranar Laraba, ta ce jami’an tsaro sun gano motar da safiyar a safiyar ranar.
Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu, ya bayyana lamarin a matsayin cin amanar aiki.
Ya kuma jinjinawa ’yan sanda bisa gaggawar da suka yi wajen gano motar da kama wanda ake zargi.
