Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cire Maryam Sanda daga jerin waɗanda aka yiwa afuwar shugaban ƙasa.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
“Bayan martanin jama’a, Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunayen waɗanda aka samu da manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, safarar miyagun ƙwayoyi, da fataucin mutane daga jerin waɗanda aka yi wa afuwa,” in ji Onanuga.
Ya ƙara da cewa an ɗauki wannan mataki ne don mutunta ra’ayoyin jama’a, inganta haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, da tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa da al’umma baki ɗaya.
Tsohon jerin sunayen da aka fitar ya haifar da cece-kuce a tsakanin jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam.
Sun bayyana matakin a matsayin amfani da ikon shugaban ƙasa ta hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan barazana ce ga tsarin shari’a.
Sun yi gargaɗin cewa sakin waɗanda suka aikata manyan laifuka zai iya ƙarfafa aikata laifi da kuma rage wa doka tasiri.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, wasu daga cikin wadanda aka riga aka yiwa afuwa a tsohon jerin sunayen, an sassauta musu hukunci maimakon a sake su gaba ɗaya.
Fadar shugaban ƙasa ta ce wannan mataki na cikin kudirin Tinubu na tabbatar da cewa afuwar shugaban ƙasa tana tafiya da adalci, tsaron jama’a da kuma kiyaye haƙƙin waɗanda abin ya shafa.
Maryam Sanda dai an yanke mata hukuncin kisa a shekarar 2020 saboda kashe mijinta, Bilyaminu Bello.
