
Falasɗinawa goma da aka saki daga tsarewar sojojin Isra’ila a zirin Gaza sun bayyana irin cin zarafin da suka fuskanta yayin da suke tsare a gidan yari.
Sakin fursunonin ya zo ne a tsakiyar rikicin da ya biyo bayan farmakin da Isra’ila ta kai a Gaza, a matsayin martani ga harin da Hamas ta kai a kudancin Isra’ila ranar 7 ga Oktoban 2023.
Tun lokacin da aka fara farmakin, Isra’ila ta tsare dubban Falasɗinawa, duk da cewa ana sakin wasu lokaci-lokaci.
Wannan ne karo farko da aka saki fursunoni tun bayan sake ɓarkewar faɗan a tsakiyar watan Maris, bayan kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas.
Mutanen goma da aka saki, waɗanda dukkansu sanye da riga mai launin ruwan toka, an miƙa su zuwa wani asibiti da ke Deir al-Balah, a tsakiyar birnin Gaza, domin samun kulawar da ta dace.
An kama su ne daga arewacin zirin Gaza a lokacin farmakin da Isra’ila ta kai a baya kafin tsagaita bude wuta a watan Janairu.
Fursunonin sun bayyana cewa sun shafe wani bangare na lokacinsu a sansanin sojan Sde Teiman, inda suka fuskanci cin zarafi da musgunawa.
Wannan sansanin sojan ya yi ƙaurin suna saboda irin tsananin da ake yi wa Falasɗinawa.