Gwamnatin Jihar Kogi, ta tabbatar da ceto mutum 24 bayan jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 200 ya kife a Kogin Neja ranar Juma’a.
Haka kuma an gano gawar mutum takwas.
Tuni aka mika waɗanda aka ceto asibiti, inda ake basu kulawa ta musamman.
Gwamnan Jihar, Ahmed Usman Ododo, ya umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, da ta tallafa wa iyalan mutanen da hatsarin ya shafa.
Sannan ya buƙaci Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, ta tabbatar da cewa an bai wa waɗanda suka kuɓuta kulawar da ta dace, kamar yadda kwamishinan yada labaran jihar Kinsley Fanwo ya ruwaito.
Hatsarin ya faru ne yayin da jirgin ke kan hanyarsa daga Kupa Ebe a Jihar Kogi zuwa Kasuwar Katcha da ke Jihar Neja.