Hadakar kungiyoyin fararen hula da kungiyoyin al’umma (CSOs da CBOs) sun bukaci Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta gudanar da bincike kan zargin badakalar kudade da ake cewa na faruwa a dukkan kananan hukumomi 27 na jihar.
Kungiyoyin, wadanda ke aiki karkashin hadin gwiwar Partnership for Inclusion of Local Governance (PILGOB), sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Sakatare Janar dinsu, Ibrahim Ilallah, ya fitar a Dutse ranar Lahadi.
A cewarsa, hadakar kungiyoyin na bibiyar rahotanni da kuma muhawarar da ake yi a shafukan sada zumunta kan zargin karkatar da kudade, cire kudade ba bisa ka’ida ba, da kuma wasu matsalolin kudi da ake zargin suna shafar tafiyar da kananan hukumomin jihar.
Ilallah ya bukaci Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Haruna Dangyatin, da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya bai wa majalisar domin tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da kudaden kananan hukumomi.
Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya bai wa majalisun dokokin jihohi damar sa ido kan tsarin gudanarwa, kudade da ayyukan kananan hukumomin da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.
A cewarsa, wannan nauyi na sa ido da majalisa ke da shi na da muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a matakin kananan hukumomi, ciki har da binciken duk wani zargin cin hanci, rashin inganci ko kuma amfani da mukami ba bisa ka’ida ba idan bukatar hakan ta taso.
Hadakar kungiyoyin ta kara da cewa idan majalisar ta dauki matakin gaggawa kuma cikin gaskiya wajen binciken lamarin, hakan zai taimaka wajen kara karfafa amincewar jama’a ga majalisar dokokin jihar.
