Kawo yanzu an binne gawarwaki 25 na wadanda hadarin kwale kwale a garin Garbi dake karamar hukumar Guru ya ritsa dasu a daren jiya, sai dai har yanzu ana dakon lalubo sauran da ba a gani ba.
Kwalekwalen ya kife da su ne a kan hanya daga garin Adiyani da ke ƙaramar hukumar Guri ta Jihar Jigawa zuwa garin Garbi a Ƙaramar hukumar Nguru ta Jihar Yobe.
Al’ummar garin Garbi dai sun ce an jima ba’a ga ibtila’in da ya girgiza garin ba kamar wannan.
Wani mazaunin yanki Ibrahim Sabo a tattaunawarsa a wakilinmu Kabir Bello Tukur ya ce an gano gawar mutane 25 daga cikin mutane sama da 40 da ake zargin sun nutse a ruwa.
A yau litinin ake sa ran cigaba da aikin neman gawarwakin ragowar mutanen da ba gano ba.
A cikin saƙon ta’aziyya, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jajanta wa iyalan da suka rasa ’yan uwansu da kuma al’ummar ƙananan hukumomin Nguru da Guri.
Ya kuma ba da umarnin a samar da duk wani tallafin lafiya da kayan aiki ga waɗanda abin ya shafa da ke karɓar magani.
