Gwamnatin Kano ta sake ƙaddamar da kula da lafiyar mata da ƙananan yara kyauta a ƙananan hukumomi 44 a karo na biyu.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin sake kaddamar da shirin a karamar hukumar Kumbotso.
Gwamnan ya ce, aikin kula da lafiyar zai dauki mako guda ana gudanar da shi domin cigaban mata da yaran Kano baki daya.
Ya kuma bukaci mata su fito da yaran su domin cin gajiyar shirin.
Sannan ya kuma yi kira ga jami’an kula da lafiya na jihar da su tabbatar da cewa sun aiwatar da shirin yadda ya kamata.
Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya kuma raba kwamfuta guda 484 domin inganta ajiye rahotanni da bayanai a asibitoci da tura bayanai da aka tara a shafukan intanet domin duniya ta gani.
Da yake jawabi kan manufofin gwamnatin na tallafawa mutanen dake fama da matsalar yunwa musamman yara da iyaye dake shayarwa, ya ce, matsalar talauci da yunwa ba iya jihar Kano ake fama da ita ba, matsala ce da ta shafi Najeriya baki daya.
Daga karshe gwamnan ya bukaci attajirai da su fito su tallafa wa mata da yara a jihar domin yaki da fatara da kuma yunwa.
