Amurka za ta ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da Najeriya ta hanyar samar da ƙarin tallafin bayanan sirri da kayan tsaro da kuma sauran kayayyakin yaƙi.
Hakan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin tawagar manyan jami’an Najeriya da jami’an Amurka, da kuma muhawarar da aka gudanar a makon da ya gabata
Hakan na kushe ne a cikin wata sanarwa da Mashawarci na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Bayar da Bayanai da Tsara Dabarun Sadarwa Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce, Amurka za ta yi hakan ne domin ƙarfafa dangantakar tsaro tsakanin ƙasashen biyu da kuma buɗe sabbin hanyoyin haɗin gwiwa da za su ƙarfafa ayyukan yaƙi da ‘yan ta’adda da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a cikin ƙasar.
Yayin ganawar da aka yi a birnin Washington, DC, tawagar Najeriya ta ƙaryata zargin kisan kiyashin da aka ce ana yiwa Kiristoci, tana jaddada cewa hare-haren tashin hankali suna shafar iyalai da al’ummomi a dukkan ɓangarorin addini da kabilu na kasar.
Babban Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu ne ya jagoranci tafiyar.
Ta kuma ta gana da manyan jami’a a ƙasar a ɓangarori daban-daban da suka haɗa da Majalisar Dokokin Amurka da Ofishin Bangaren Addinin Fadar White House da Ma’aikatar Harkokin Waje da Majalisar Tsaro ta Ƙasa, da kuna Ma’aikatar Yaƙi.
Sauran ‘yan tawagar sun haɗa da Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi; Shugaban Ma’aikatan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Shugaban Sashen Leken Asiri na Tsaro, Laftanal Janar Emmanuel Undiandeye; Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun da kuma wakilai biyu daga Ofishin Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Ƙasa.
