Daga Fatima Hassan Gagara
Amurka ta haramtawa Wole Soyinka fitaccen marubuci ɗan Najeriya shiga kasarta.
Soyinka wanda ya taɓa lashe kyautar Nobel ta duniya, ya ce gwamnatin Amurka ta soke bizarsa tana mai haramta masa shiga ƙasar.
Farfesa Soyinka ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ya kira a Legas a ranar Talata
“Ba ni da biza; an haramta min shiga Amurka. Saboda haka idan kuna son ganina, kun san inda za ku same ni,
“Ba ni da wani tarihin aikata laifuka a baya ko ma babban laifi ko rashin ɗa’a da zai sa in cancanci a soke min biza.
Soyinka ya ce, dole ce ta sa ya kira wannan taron saboda mutanen Amurka da ke tsammanin halartar wasu taruka a can. Ya kuma ce kar su ɓata lokacinsu. Sun sann in da za su same shi
Fitaccen marubucin ya kuma ce, Ofishin Jakadancin Amurka ne ya sanar da shi batun ƙwace bizar a wata wasiƙa da ya aike masa.
Sai dai ya sanar da cewa ba shi da masaniya kan wani mummunan laifi da ya aikata da har zai sa Amurkan ta soke bizar da ta ba shi.
Har yanzu dai hukumomin Amurka ba su fitar da wata sanarwa kan dalilin sokewar bizar Farfesa Wole Soyinka ba.
