Amurka ta buƙaci ‘yan kasarta da su ƙauracewa yin balaguro zuwa Jamhuriyar Nijar, ƙasar da ta ce na fama da matsalolin masu tayar da ƙayar baya, da kuma masu garkuwa da mutane haɗi da sauran manyan laifuka.
Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar a ranar Juma’a.
Matakin na zuwa ne, bayan mako guda da yin garkuwa da wani Ba’amurke da aka yi a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar din.
Sanarwar ta kuma umarci dukkanin Amurkawan da ke zaune a ƙasar, da su yi gaggawar ficewa, domin kaucewa faɗawa hannun masu riƙe da makamai.
Rahotanni na cewa, ‘yan kasashen Turai da dama aka yi garkuwa da su a wannan kasa da ke yankin Sahel a bana kaɗai.
